top of page

Tambayoyi Da Akafi Tambaya.

GET IN TOUCH

We'd love to hear from you

1. Menene SANU?

SANU manhajar siya da siyarwar Zinare da Azurfa. Manhajar Sanu yanada nashi Nau'in kudi na dijital , dake amatsayin Sanu-GLD (SNG) Sanu-SLV (SNS) wanda yake a matsayin Zinare da Azurfa na zahiri. Takaitaccen bayani shine, manhaja ce wanda yake bada damar mallakar asusun Zinare da Azurfa a saukake. Zaka iya gani ajiyarka na cikin asusun kuma da tabbacin kanada Zinare ko Azurfa a zahirance a yayinda kayi siyayya. Idan har ka zabi ka karbi samfurinka, kanada zabi a cikin jerin samfura da muke dasu sannan ka shirya dauka a daya daga cikin zababbun rassan karbar samfari.

2. Menene SANU yake nufi?

Sanu yana nufin ‘zinariya’ a yaren Bambara na ƙasar Mali.

3. Menene Sanu-GLD?

Sanu-GLD yana wakiltar gram ishirin na Zinare.

4. Menene Sanu-SLV?

Sanu-SLV yana wakiltar gram hamsin na azurfa.

5. Wadanne samfura ake samu don fansa na zahiri?

Ana samun samfuran LBMA* don fansa a Najeriya.  Sauran samfuran daga

OECD ** ana samun madogaran masu yarda don fansa a cikin UAE.

*Kungiyar Kasuwar Bullion ta London

**Kungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziƙi da Ci Gaba

6. A ina za’a iya karbar Zinariya ko Azurfa na zahiri?

A Najeriya, ana iya karba a zababbu rassan bankin Union Bank.

A Dubai, a kantin cikin Gold Souk.

Yen kungiyar Gold Club a Nigeria zasu iya samun damar karbar Zinare ko Azurfa a asusun ajiyar mu.

7. Menene Gold Club kuma ta yaya zan yi rajista?

Kungiyar Gold Club kungiya ce ga abokan cinikin mu waɗanda ke neman siyan fiye da kilo daya na zinare kuma sun kasance amintattun abokan cinikayya.  Bayan tantancewa da amincewa, abokan ciniki za su samu sararin ajiya a cikin akwatunan ajiya mai aminci da tsaro a wuraren abokan hulɗarmu.

8. Idan ba na son karbar zinare ko azurfa fa?  Dole ne in fanshi Sanu-GLD ko Sanu-SLV a zahiri?


Ba dole ba ne ka karba a zahirance.  Kuna iya ajiyewa da adanawa tare da mu daga ko'ina cikin fadin duniya kuma ku sayarwa cikin sauki a duk lokacin da aka shirya.

9. Zan iya karbar samfurana a wasu ƙasashe?


A halin yanzu kuna iya fansa da ɗaukar samfur na zahiri kawai a cikin Najeriya da UAE.  Muna sa ran samun wuraren da za a iya ɗauka a wasu ƙasashe nan ba da jimawa ba.

10. Menene mafi ƙarancin zinari ko azurfa da za'a iya siya akan app ɗin Sanu?

Mafi qarancin siyan a Sanu app shine $0.25 ko N100.00

11. Menene bambanci tsakanin siyan Sanu-GLD da siyan zinariya ETF?

Siyan Sanu-GLD iri ɗaya ne da siyan Zinare a zahiri saboda Sanu-GLD yana goye a bayansa ɗaya bisa ɗaya na zinare a zahiri kuma ana iya fansa a amsa a zaɓaɓɓun rassan bankunan Union Bank.  Don haka Sanu yana ba da damar samun zinare a cikin nau'in dijital kuma a karba a zahirance.

12. me karancin lokacin da zan iya siyarwa akan Sanu bayan siya?

Bayan tantancewa da amenicewa ana iya siyar da Sanu-GLD da Sanu-SLV a cikin sa'o'i 24 bayan siya.  Za a mayar da samfuran da aka fansa zuwa rashen da aka karba, a dawo dasu cikin mallakarmu kafin a ƙirƙira matakin da za’a biya a manhajar Sanu.

14. ta yaya zan iya karban zinariya ko azurfa bayan siya?

Ba dole ba ne ka ɗauki zinare ko azurfa bayan siya. Idan har anason amsar samfur na zahiri:

A cikin manhajar sanu, a zaɓi samfur, sai a siyi samfur, zaɓi rashen bankin da akeso a ɗauka.  Za a aika maka da umarni ta hanya email yadda za’a karba cikin sauki .

15. Ta yaya zan iya sanin farashin zinariya da azurfa na yanzu akan Sanu app?

Yanayin farashin Sanu yana bibiyan farashin kasuwar LBMA na duniya.  Sanu-GLD daya da Sanu-SLV daya, suna wakiltar gram ishirin na zinari da gram hamsin na azurfa bi da bi.  Ana iya duba farashin Sanu akan allon dake cikin manhajar.

17. Yaya ake kula da aike?

Abokan hulɗar aikin mu suna isar da samfura cikin aminci da tsaro zuwa zababbun rassa.  A sani cewar isowar samfura zuwa wasu rassa yana daukan lokaci, wasu wuraren bazai samu nan ta ke ba.

16. Shin duk samfuran farashinsu iri ɗaya ne?

Farashin samfurin ya bambanta dangane da iri, girma, inganci da ƙirar samfur.  samfuran LBMA suna da mafi girman kima a kasuwar zinare ta duniya.  A Najeriya, suna zuwa da ƙarin VAT da harajin shigo da kaya. Zinariyar Sanu na dijital farashinsu yana ƙasa da samfuran LBMA na zahiri.  Sauran kayayyakin da ba LBMA ba da ake samu a Dubai suma suna da nasu kimar amma ba su da daraja kamar samfuran LBMA.  A cikin Dubai, samfuran suma ba sa jan Karin kudi saboda VAT da harajin Shigo da kaya, za’a samu rangwamen farashi.

18. Yaya ake sarrafa adana da ajiya?

Asusun Ajiyar da kudin inshore an sharhintasu akan farashin Sanu-GLD da Sanu-SLV sannan muka mallakar asusun zahiri na Sanu.  Ga yen kungiyar Gold Club na Najeriya, suna iya adana kadarar su a cikin akwatunan ajiya na amintattun abokan huldarmu.

19. Wane kudade ne da za ayi la'akari dasu?

Kankanin kamashon siya da siyarwa, harajin ƙirƙiran token, da harajin koda kaya ya samu matsala.  harajin musayanyawa da kuma inda  yuwuwar VAT da harajin shigo da kaya.

20. Yaya ake sayayya akan manhajar Sanu?

Ana siyan duk samfuran da tsabar Sanu.  Sanu-GLD ko Sanu-SLV ana siyan su kai tsaye daga manhajar Sanu. Bayan shimun asusu tare da haɗawa da amintaccen asusun banki na Fiat ko wasu katunan kuɗi.  Hakanan ana iya aikawa da tsabar sanu a cikin Sanu manhajar daga asusu zuwa wani asusun.

21. Menene mafi yawan Sanu-GLD ko Sanu-SLV da za'a iya siya a rana?

  - Ya danganta da matakin sanin abokin cinikinmu:

     • Giram dari na zinare ko kilo daya na azurfa

     • kilo na zinariya ko kilo biyar na azurfa

Samun damar mallakar sanfura mai yawa yana samuwa kawai ga yen kungiyar Gold Club waɗanda suka wuce ingantattun tacewa da sanayya abokan cinikin.

22. Abubuwan da ake bukata dan tantancewar abokan cinikanmu?

Tare da kowane mataki akwai ƙarin bayanai da matakai da ake bukata na abokan cinikinmu:

  • karamin Mataki na farko

   i.  Gram daya na zinare ko nauyin OZ biyu na azurfa a rana

   ii.  Suna, Email, lambar waya, BVN*, wakilci wani makusanci

   • Matakin na daya

   i.  Gram goma na zinare ko kilo daya na azurfa iyaka a rana

   ii.  Tabbatar da lambar waya, zababben katin shaida, Adireshi

   • Mataki na biyu

   i.  Gram dari na zinare ko kilo biyar na azurfa a rana

   ii.  Tabbatar hoton fuska, Tabbatar da adireshi

   • Mataki na uku

   i.  kilo daya na zinare ko kilo goma na azurfa a rana

   ii.  Fasfo na kasa da kasa, Tushen samun kudade, tantancewa daga AML/CFT

   • Yen kungiyar Gold Club

   i.  Idan an nema kuma an cika ka’idojin mataki na uku

*Don yen Najeriya ko mallaka na zahiri a Najeriya

23. Yaya tsawon lokacin da ake ɗauka don dawo da kuɗi da cinikin da bai yi nasara ba?

Ya danganta da asalin bankin abokin ciniki, warwarewa da maidowar kudaden da basuyi nasaran ciniki ba yakan dau kwana uku zuwa biyar na kwanakin aiki.

24. Menene ka’idojin dawowa da samfurin da aka karba?

Muna karɓar samfurin da abokin ciniki wanda ya sayi samfurin ya dawo mana dashi ne kawai.  Idan ba a buɗe kunshin ba, za a mayar da cikakken kuɗi cikin sa'o'i 48.  Duk sauran ƙimar dawo da kuɗi sun dogara da yanayin dawowar samfurin kuma tabbas mafi cancantar kuɗin zai zama darajar zinare.  Za a ƙididdige duk abin da aka dawo a cikin kwanakin aiki biyar.

25. Shin akwai ƙarin farashin akan mai fansar Zahiri?

Ya Danganta da ƙasar da kake, ana iya biyan VAT da harajin shigo da kaya.

26. Shin Sanu app yana samuwa a duk ƙasashen duniya?

Manhajar Sanu duk duniya yake kuma ana iya daukoshi a Apple store da google playstore.

27. Zan iya kasuwanci a kan Sanu app?

Manhajar Sanu shafi ne mai bada daman, siye da siyarwar zinare da azurfa yayin kiyaye fa'idar samun asusun kudin dijital tare da samun cikakkun bayanai game da kudin da aka mallaka a kowane lokaci. Manhajar  Sanu baya bada damar cinikayya.

28. Yaya ake  ƙayyade farashi Sanu?

Hanyoyin farashi tare yana tafiya hannu da hannu ne  da farashin kasuwannin duniya tare da wasu bambance-bambancen da aka ƙirƙira don lura da farashin ma’adanan kasa masu daraja.

29. Shin Sanu yana ba da izinin ciniki tareda wakilci?

Abin takaici, ba za mu iya karɓar ma'amala da wakilci ba saboda dokokin AML/CFT na ƙasashen duniya.

30. Yaya ingancin tsaron manhajar Sanu yake?

Shahararriyar ƙungiyar fasaha ce ta kirkiri manhajar Sanu tare da ingantacciyar tsaro na samfuran kudin dijital masu haske da aminci.  Sassan Sanu ya ƙunshi ingantaccen tsaro. Babban kamfani na smart blockchain ya samu bincike da lura daga babban kamfanin duba diddigin bayanai.  Amma a sani cewa kare bayanai na sirrinka yana da mahimmanci ga tsaro na manhajar da asusunka.

31.Shin zinarina da azurfata lafiya tare da Sanu?

Ee, karafa masu tamani suna da tsaro kuma suna da cikakken inshora a hannunmu.  Ƙarfe masu daraja suna ɓoye a cikin rumfuna masu zaman kansu da yawa tare da sa hannun ma'aikatan gandun daji na ƙasa da ƙasa masu zaman kansu da amintattun kamfanonin dabaru.

32. Ta yaya zan bayar da korafi gameda manhajar Sanu?

Idan kun ci karo da wata matsala tare da manhajar Sanu, a tuntuɓi support@sanucoin.com za mu amsa daidai cikin sa'o'i shida zuwa takwas.

33. Ta yaya zan warware matsalar tare da odar samfuri na?

Idan kun ci karo da kowace matsala tare da odar samfuran ku, a tuntuɓi support@sanucoin.com za mu amsa daidai cikin sa'o'i 6-8.

34. Ina ofisoshin ku yake?

Ofisoshinmu yana yankin wararren yankin Kasuwancin dake filin jirgi na Murtala Muhammed International Airport Lagos Nigeria da DMCC a Dubai.

35. Zan iya sayar da zinare na a manhajar Sanu?

A halin yanzu muna siyan samfura waɗanda muka siyar ta hanyar Sanu don kare ƙaƙƙarfan asalin sanfuranmu.

36. Shin Akwai kudade na ɓoye akan Sanu?

Farashin a Sanu a bude yake kuma tsayayye.  Bambance bambancen farashi da kudade sun danganta da samfur da ƙasar fansar samfur a zahiri.

37. Zan iya siyarda Sanu-GLD da Sanu-SLV a farashin dana siyesu?

Farshin siyarda Sanu-GLD da Sanu-SLV yana dogara akan farashin zinare a kasuwar duniya. Bazaka iya siyar dashi a farashin da aka siya ba.

38. Zan iya karbar Zinare da azura a wani magudanar banda banki?

Yen kungiyar Gold Club a Nigeria zasu iya samun damar karbar Zinare ko Azurfa a asusun ajiyar mu. Abokan jinikin zasu iya karbar nasu Zinaren da Azurfa a wasu zababbun cibiyar Union Bank.

Kasar dubai kuma akwai damar karbar Zinare da Azurafa a sassa daban daban na kasar ba tare da zuwa banki ba. Amma wasu sassan karbar Zinare da Azurfa a kasashen duniya suna nan tafe.

39. Zan iya sauya Zinare da Azurfa dana nemi na karba?

Zamuyi la’akari da wadataccen Zinare da Azurfa da muke dashi a reshen karba daka zaba, a tsakanin awa 24 da ka nemi ka karbi Zinare da Azurfarka. A tuna da cewar farashin zai iya banbanta. Misali, zamuyi la’akari da farashin Zinare da Azurfar da aka sauya.

40. Tayaya zan dinga bibiyar jigilar zuwan Zinare da Azurfa dana siya?

Duk da cewar bama aikawa da kaya inda mutuum yake, Zinare da Azurfa zasu zama a wadace a wasu zababbun rassan Union Banka fadin Nigeria da kuma a kasar Dubai. Amma za’a iya bin diddgin da matsayin da Zinare da Azurfar ke ciki a manhajar Sanu da kuma hanyar sadarwa ta hanyar Email akan duk canjin dake gudana akan kayanka.

41. Zan iya sauya reshen karbar kayana?

Duba da wadataccen kaya, zamu bada damar canjin rashen daukan kaya idan har an nemi canjin reshen a tsakinin awa 24 na karban kayan.

42. Mai zai faru da saura ragowar canjin Sanu-GLD da Sanu-SLV bayan na karbi gundarin Zinare ko Azurfa.

Raguwar Sanu-GLD da Sanu-SLV da bai kai matsayin daya daga cikin kayan mu ba, zai zauna a cikin asusunka na manhajar Sanu. Amma idan kaso, zaka iya maidashi zuwa kudi.

43. Zan iya musanya Sanu-GLD zuwa Sanu-SLV?

A yanzu babu damar musanyawa a tsakanin Sanu-GLD da kuma Sanu-SLV, amma zaka iya siyar da daya daga cikinsu sannan kuma sai ka sayi daya daga cikinsu.

44. Wasu nau’in kudi ne akwai a cikin manhajar Sanu?

Manhajar Sanu yana karbar ko wanne nauy’in kudi idan har anada katin kudi ko ayi turin kudi daga banki. Kudin ka aka tsara akan farashi da cikiniki akan mahajar sune Dalar Amirka Nairar Nigeria.

45. Me zai faru idan na sauya wayana na kuma dauko manhajar Sanu?

Asusun bazai samu matsala ba. Kawai a dauko manhajar sanu sai a sanya bayanai, a ci gaba da siyyayya a inda aka tsaya.

46. Tayaya zan duba tarihin mu’amalar ciniki?

Akan manhajar Sanu, a zabi tarihin ciniki za’aga tarihiri da mu’amalar cinikayya.

47. Shin zan iya biyan kudin Zinare da Azurfa har tsawon wani lokaci?

Tabbas. Sanu yana bada damar siyan Zinare da Azurfa kadan kadan har na tsawon lokacin da zai kai kwatankwacin yadda za’a iya amsar gundarin Zinare da Azurfa a zahirance.

48. Yaya ake daidaita lissafin asusu da wallet?

Tare da duk samfuran da ke kan blockchain kuma tare da kwararraun ingantattun gudanarwar ma’ajiya, biyan kuɗi zuwa wallet din Sanu yana faruwa a cikin mintuna kaɗan.  Tura kudi ta hanyar amintaccen asusun banki na Fiat yana dogarone akan bankin cininki kuma yakan iya daukan sa’o’i 48.

48. How do I buy other types of gold or silver on SANU?

To buy LBMA and other types of gold or silver on the app, see below

Step 1: Tap the "gold bar" button (It is the second button from the left at the bottom of the app)

Step 2: Confirm the "total cost", i.e how much SNG or SNS is required 

Step 3: If you have the required amount of SNG or SNS, tap "Confirm purchase

To buy SANU Gold/ Silver (SNG/ SNS), see 19 above. 

Send us an email to support@sanucoin.com

We typically respond quickly.

  • Instagram
  • Twitter

Or reach out to us on social

Cant find the answer you are looking for? then

bottom of page